Rahoto: Yadda Aka Gudanar Da Jarrabawar Post-UTME A Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano
A yau (Alhamis) 14 ga watan Satumban 2023 ne, Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Kano (Northwest) ta gudanar da jarrabawar gwajin gaba da UTME (Post-UTME) ga dubban ɗaliban da ke neman Makarantar, a kakar karatu ta 2023/2024.
An gudanar da jarrabawar ta rana gudana ne kuma ga dukkannin Ɗaliban da ke neman guraben karatu a Sassan Karatu (Departments) ɗin Jami’ar guda 43.
Wakilin Rariya Online, Miftahu Ahmad Panda, wanda ya halarci wuraren rubuta jarrabawar, ya shaida mana cewar, an gudanar da jarrabawar ne cikin rukuni biyu, wato rukunin ƴan Safiya (8:00 zuwa 10:00), da kuma na rana (12:00 zuwa ƙarfe 2:00), inda aka ware ɗaliban da ke neman kowanne sashe (Department) wuri guda.
Ka zalika, Shuwagabannin ƙungiyar ɗalibai ƴan asalin jihar Kano (NAKSS) da ke karatu a makarantar, ƙarƙashin Jagorancin Comrade Habiba (Garkuwar Ɗalibai), sun gudanar da Aikin nunawa ɗalibai, da ma raka wasu daga cikinsu, zuwa wuraren rubuta jarrabawoyin nasu.
A nata ɓangaren, ita ma hukumar makarantar ta yi ƙoƙarin kiyaye lokaci, a ya yin gudanar da jarrabawar.
Bayan fitowa daga jarrabawar kuma, mun tattauna da wasu ɗalibai inda su ka ce jarrabawar ta yi matuƙar sauƙi, kuma su na da kyakykyawan fatan samun nasara, ya yin da wani rukunin kuma su ka bayyana yin tsaurinta.
Bisa al’ada dai, sakamakon jarrabawar ba ya shallake makon farko daga lokacin da aka rubuta ta, zuwa fitowarsa.