Rahotanni

Rahoto: Yadda Aka Rantsar Da Abba Gida-Gida, A Matsayin Gwamnan Kano

Da safiyar yau (Litinin), 29 ga watan Mayun 2023 ne, aka gudanar da bikin rantsar da sabon Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da Mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam, a buɗaɗɗen Filin Wasa na Sani Abacha Stadium, da ke ƙofar Mata.

Wakilin Rariya Online, Miftahu Ahmad Panda, wanda ya halarci bikin rantsuwar, ya rawaito cewar, taron ya samu halartar manyan baƙi daga ciki, da wajen jihar Kano, waɗanda su ka haɗarda Jagoran ɗarikar Kwankwasiyya, kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa, na jam’iyyar NNPP, a zaɓen da ya gabata, Rabi’u Musa Kwankwaso, da Mataimakinsa, Ihadosa, Buba Galadima, Zaɓaɓɓun Sanatocin Jam’iyyar ta NNPP, Zaɓaɓɓun ƴan Majalissun tarayya, Zaɓaɓɓun ƴan majalissar jiha, Sarakunan Kano na yanka, masu daraja ta ɗaya, da ma Shuwagabanni da membobin kwamitin karɓar mulki.

Sauran sune Manyan jaruman masana’antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood), Mawaƙa, Jaruman Tiktok, da ma masu bayar da dariya (Comedians).

Sai dai, cincirindon jama’ar da aka samu, ya kawo tasgaro ga yunƙurin gudanar da da al’adar faretin da aka saba gudanarwa, a duk lokacin da aka rantsar da sababbin Shuwagabannin.

Bayan kammala gudanar da wannan bikin rantsuwa kuma, Gwamnan ya wuce kaitsaye zuwa wasu muhimman wurare, inda ya fara kai ziyarar Aiki.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button