Rahoto: Yadda Alhaji Sani Zangina Ya Hana Ƙwacewa Dattijo Gidansa, A Maraba
Fitaccen Ɗan Jaridar nan, mai gudanar da ayyukan jin ƙan al’umma, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya yi nasarar hana ƙwacewa wani dattijo mai shekaru 92 gidansa, da ke yankin Maraba, a jihar Nasarawa.
Tun da farko dai, dattijon ne ya miƙa kokensa ga Alhajin, wanda ke cigaba da zamowa baya goya marayu, kuma gatan marasa gata da marasa ƙarfi, cewar ana barazanar ƙwace masa filinsa.
Hakan ne kuma, ya sanya Alhajin bazama, tare da shan alwashin sanya hannu cikin lamarin, da niyyar taimaka masa, kamar yadda ya wallafa, a shafinsa na Facebook.
“Wani dan shekara 92 da haihuwa ya kawomin karar za’a kwace masa gida a Maraba.
“Shima zamu taimaka masa.”, a cewar Alhajin.
Sai dai, bayan miƙa katinsa, tare da buƙatar a kaiwa dukkannin wanda aka ga dama, mutumin da ke shirin turmushe wannan gida ya sha jinin jikinsa, tare da mayar da katin ga, Alhaji Sani Ahmad Zangina, wanda shi ne ya damƙa katin, tun a karon farko.
Baya ga haka kuma, mutumin ya bayyana cire hannunsa daga cikin lamarin, tare da barwa dattijon gidansa, kamar yadda Alhaji Sani Ahmad Zanginan dai, ya sake wallafawa a shafinsa na Facebook, da yammacin Lahadi.
“Ga katina ku kai duk inda kukaga dama, sai suka kawomin katin.
Daga karshe dai yace ya cire hannunsa kuma gidansu an bar masu.”, a cewarsa.
Ba kuma wannan ne karo na farko, da Alhaji Sani Ahmad Zanginan ke tsoma hannu cikin al’amuran ƙwato haƙƙoƙin masu ƙaramin ƙarfi da gajiyayyu ba.