Rahoto: Yadda Bikin Karrama Gwarazan Gasar Hikayata Ya Gudana
Da yammacin yau (Alhamis), 30 ga watan Nuwamba ne, aka gudanar da bikin karrama Gwarazan Gasar Hikayata, wacce kafar yaɗa Labarai ta BBC Hausa, ke shiryawa a kowacce shekara, ga Marubuta Mata Zalla.
Wakilin Rariya Online, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya rawaito mana yadda taron na bana, wanda ya gudana a babban birnin tarayya Abuja ya samu halartar manyan baƙi daga sannan Najeriya, har ma da Maƙwabtan ƙasashe.
Daga cikin waɗanda su ka samu halartar bikin, akwai Sarkin Katagum, Alhaji Umar Faruk II; Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura; Farfesa Abdallah Uba Adamu – na Jami’ar Bayero; Sanata Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila – wanda ke wakiltar kudancin Kano a Majalissar Dattijai; har ma da Salihu Tanko Yakasai, da ya yiwa jam’iyyar PRP takarar kujerar Gwamnan jihar Kano, a babban zaɓen 2023 da ya gabata.
Sauran manyan baƙi a taron su ne: Uwargidan Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje; Uwargidan Gwamnan Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Radda, Ƴan Jaridu, har ma da dandazon sauran al’umma.
Marubuciya Aisha Adam Hussaini ce dai ta zo ta farko a gasar, da labarinta mai taken ‘Rina a Kaba’, inda ta rabauta da kyautar Naira miliyan guda.
Sai Aisha Abdullahi Yabo, da ta zo ta biyu, da labarinta mai taken ‘Baƙin Kishi’, inda ta rabauta da kyautar Naira 750,000.
Aisha Sani Abdullahi kuwa, ta uku tazo, da labarinta mai taken ‘Tuwon Ƙasa’, inda ta yi nasarar rabauta da kyautar zunzurutun kuɗi har Naira 500,000.