Nishaɗi

Rahoto: Yadda Kalaman Fitsara A Waƙa Su Ka Sanya Kotu Bada Umarnin Daƙume Ado Gwanja

Da tsakar ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairun da mu ke bankwana da shi ne, Babbar Kotun Jihar Kano, mai lamba 5, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a, Aisha Mahmud, ta bada umarnin kama fitaccen Mawaƙin Masana’antar Shirya Fina-Finan Hausa (Kannywood), Ado Isa Gwanja, tare da haramta masa Rera Waƙa, har sai Jami’an Ƴan Sanda sun kammala bincike akansa.

Majalissar Malaman Kano ce kuma, ta maka Mawaƙin Ƙara a gaban Kotu, bisa zarginsa da furta kalaman fitsara a cikin waƙoƙinsa.

Nasan mai bibiyar Rariya Online, shaidane kan yadda Ado Gwanjan ke furta zage-zage a cikin baitocin waƙarsa, ba ya ga kalaman fitsara da ya ke yi da sunan salon magana, musammanma a baya-bayan nan da ya fara rera waƙoƙin habaici.

Idan ba a manta ba kuma, ko a baya sai da hukumar kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasa (NBC) ta haramtawa gidajen Rediyo da Talabijin ɗin da ke faɗin ƙasar nan sanya waƙarsa mai taken ‘War!’, bayan tsintar zage-zage da kalaman fitsarar da ke ƙunshe a cikin waƙar.

Abin jira a gani dai, bai wuce ko wannan lamarin ka iya sanya Ado Gwanjan yin gyara a salon waƙoƙin da ya ke rerawa, ko kuma zai Ari rigar naƙi ya rataya.

Har zuwa lokacin da mu ke haɗa muku wannan rahoto kuma, Mawaƙin bai ce ko uffan, game da umarnin Kotun ba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button