Ilimi

Rahoto: Yadda Kwalejin Kiwon Lafiya Ta Jami’ar Bayero Ta Gudanar Da Bikin Yaye Ɗalibai

Kwalejin Kimiyyar Lafiya (College Of Health Sciences) ta Jami’ar Bayero, da ke birnin Kano, ta gudanar da bikin yaye Ɗaliban da su ka kammala karatunsu, a Jami’ar, a fannonin Aikin Likitanci mabanbanta, yau (Alhamis), a babban ɗakin taro na Convocation Arena.

Nau’o’in Likitocin da Jami’ar ta ya ye dai, sun haɗarda Likitocin Idanu (Optometrists), Likitoci Masu Aikin Gwaje-Gwaje (Medical Laboratory Scientists), Likitoci masu ɗaukar hoton cututtuka (Radiographers), Likitocin Jinya (Nursing Scientists), har da ma Likitocin gashin ƙashi (Physiotherapers).

Da ya ke jawabi a ya yin taron, Shugaban Jami’ar ta Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas, wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa, bayyana farincikinsa ya yi bisa gagarumar nasarar da Jami’ar ke cigaba da cimmawa, tare da buƙatar sababbin Likitocin da su kasance masu ƙwazo da nuna jajircewa, a duk inda su ka tsinci kansu.

A nata ɓangaren, Farfesa Aisha Kuliya Gwarzo, ta Kwalejin Kiwon Lafiyar, taya sababbin Likitocin murna ta yi, tare da ƙarfafa musu gwuiwa kan yin aiki cikin jajircewa a kuma dunƙule; kafaɗa da kafaɗa da ƙwararru a fannoninsu.

A ƙarshen taron kuma, an karrama jajirtattun Ɗaliban da su ka nuna bajinta, a zangon karatun da su ka shafe, tun daga shekarar 2017 zuwa Dubu Biyu Da Ashirin Da Ukun da mu ke ciki.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button