Rahotanni

Rahoto : Yadda Masu Ruwa Da Tsaki Ke Hana Kasuwar Muhammadu Buhari Rawar Gaban Hantsi

A cigaba da kawo maku halin da Kasuwar Shugaba Muhammadu Buhari International Market dake garin Mararaba a karamar hukumar Karu a Jahar Nasarawa.

Wannan Kasuwa dai Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da ita a shekarar 2018 inda aka maye gurbinta da sunanshi.

A wani bincike da Jaridar Karamchi ta kaddamar na kusan shekaru 5, ta gano cewa akwai masu ruwa da tsaki a Jahar dake kawo tasgaro na hana wannan Kasuwar rawar gaban hantsi, saboda bukatar kansu da iyalansu.

Irin wadannan shuguna dai sun kai sama da dubu biyar (5k) inda suke ci gaba da zaman kashe wando ba tare da nemawa Jahar ko karamar hukumar Karu komi ba, duk da irin halin talauci da rashin aikin yi da ya addabi Najeriya.

Wasu Jama’ar dai na ganin akwai yuwar farfado da kasuwar nan da wani lokaci kadan bayan kaddamar da gwamna a karo na biyu.

Zamu kawo maku hira ta musamman da Shugaban Kasuwannin Jahar Nasarawa baki day Mr. Yakubu Uban Gari da zarar mun samu damar hakan.

Ku dakace mu yayinda muke dakon ra’ayouinku kan wannan rahoton.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button