Ranar Hausa: KO KUN SAN GIRMAN HARSHEN HAUSA ?
–Na Ɗaya: Aƙalla mutane miliyan ɗari-da-hamsin ne ke magana da harshen Hausa a faɗin duniya
—Na Biyu: A cikin mutane sama da biliyan takwas da ke magana da harsuna sama da dubu-bakwai a faɗin duniya, Hausa shi ne harshe na ashirin-da-bakwai cikin manyan harsunan duniya
—Na Uku: A cikin harsuna sama da ɗari-biyar a ƙasar Nijeriya, Hausa shi ne harshe na ɗaya da aka fi amfani da shi
—Na Huɗu: A cikin harsuna sama da dubu-biyu a faɗin nahiyar Afirka, Hausa shi ne harshe na biyar da aka fi amfani da shi
—Na Biyar: Ana koyar da harshen Hausa a manyan jami’o’i a faɗin duniya kamar a ƙasar Burtaniya, Sin, Jamus da sauransu
—Na Shida: Wanzuwar harshen Hausa a duniya ya haura shekaru dubu
—Na Bakwai: Ana amfani da harshen Hausa wajen fassara hudubobi a masallacin Annabi (SAW) da ke ƙasar Saudiya
—Na Takwas: Manyan Turawa suna karantar harshen Hausa, sannan sun yi rubuce-rubuce da dama a kansa
—Na Tara: Ana amfani da harshen Hausa wajen fassara a manyan kamfanoni fasahar zamani kamar su Google, Facebook, WhatsApp, da sauransu
—Na Goma: Ana amfani da harshen Hausa a manyan gidajen jaridun duniya kamar su BBC (Burtaniya), VOA (Amurka), RFI (Faransa), TRT (Turkiyya), CRI (Sin), da DW (Jamus)
Allah Ya ƴara ɗaukaka harshen Hausa, Ya samar da dawwamamman zaman lafiya da cigaba da mai ɗorewa a ƙasar Hausa da kewayenta bakiɗaya, amin.
Ina matuƙar farin cikin kasancewata Bahaushe tare da cikakken alfahari da harshena.
—Muhammad Auwal Ahmad.