Ranar Hausa: TARIHIN ASALIN HAUSAWA
Tarihin Asalin Hausawa ya kasance babban al’amari wanda yake bukatar nutsuwa sosai. Hausawa sun kasance wata al’ummar bakaken fata wadda take zaune a yankin arewacin Nigeria ta yanzu da kuma kudancin kasar Niger ta yanzu. Hausawa sun kasance suna yin magana da harshen Hausa wanda yake daya daga cikin mafi yaduwar harsunan bakaken fatar Arewa.
Haka kuma Hausawa sun kasance al’umma masu kwazo wadanda suka shahara da yin fatauci da kuma yin kasuwanci. Sannan kuma akalla kaso 95% na al’ummar Hausawa musulmi ne masu bin addinin musulunci.
Asalin Hausawa
An samu sabani akan Tarihin Asalin Hausawa tsakanin malamai da dama masu nazarın asalin Hausawa na tarihi da rubuta shi, da kuma masu tarihin baka mafi dadewa da tasiri na Tarihin baka na Bayajidda mijin Sarauniya Daurama.
Don haka ne aka samu bayanai daban-daban akan tarihin asalin Hausawa. Ga wasu daga cikin bayanan.
HAUSAWA DAGA MISRA SUKE
Wasu daga cikin masana masu binciken tarihin kasar Hausa sun alakanta tarihin asalin Hausawa da yankin Mısra wato kasashen da suka hada da kasashen Egypt, arewacin Sudan, Libya, da kuma Palestine na yanzu.
Daya daga cikin manazartan wato Lugard a cikin littafin sa ‘A Tropical Dependency’ yace Hausawa sun fito be daga cikin kabilar Kibdawan Misra. Ya Kuma kara da cewa Hausawa da harshen su sun samo asali ne daga suna Fir’auna Hausal kakan Fir’auna Namarudu.
HAUSAWA DAGA HABASHA SUKE
Wasu Kuma daga cikin masana tarihi wadanda suka nazarci tarihin asalin Hausawa sun ce Hausawa sun fito ne daga yankin Habasha wato kasar Ethiopia a yanzu.
Masana da suka samar da wannan bayani sun ce kabilar Hausawa na farko da suka sauka a yankin kasar Hausa sun kasance maharba ne wadanda ake ganin sun taso ne da yankin gabashin Africa musamman yankin Habasha. Manazartan sun ce al’adun Hausawan farko musamman ta bangaren addini, sutura, da kuma wasu kalmomi harshe sun kasance suna da kamanceceniya da na wasu mutanen yankin Habasha. Misali, kabilun Hausawa na farko sun kasance suna bautawa rana wanda ya kasance addinin da mutanen Habasha suka fi shahara akan sa. Har Yau Har Gobe Da Akwai Hausawa A Habasha
HANGEN WASU MASANAN
Saidai Farfesa Tijjani Muhammad Naniya, wani masanin tarihi da al’adun Hausa a jami’ar Bayero da ke Kano ya bayyana cewa:
“Hausawa wani jinsi ne na jama’a da suka samu kansu mafi yawa a yammacin Afrika, mutane ne da suka kafa garuruwa daban-daban, sannan duk garin da suka kafa suna da jagoranci na sarautarsu.
Ba su samu damar hada kansu wuri guda karkashin tuta daya ba, hakan ya sa ake kiran kowanne da sunan garinsu da kuma sunan sarautarsu.
Abin da ya zo ga tarihi, kasar Hausa na da manyan garuruwa guda bakwai wato inda suka fara zama, wadannan garuruwa sun hadar da Daura da Gobir da Kano da Katsina da Zazzau da Rano da kuma Birom.
Fitaccen masanin tarihin Hausawa, Farfesa Abdullahi Sa’id da almajiransa kamar Farfesa Mahadi Adamu, sun bayyana cewa “asalin Hausawa sun taho ne daga yankin Arewacin jamhuriyyar Nijar, wajen Agadas a yanzu, lokacin da Hamada ta fara buwaya sai neman waje mai danshi da lema da ruwa ya sa wasunsu suka fara sauya matsuguni” suka rika komawa wadancan garuruwa da aka lasabta a sama da ke Najeriya.
“Wadanda suka fara kafa tarihi a cikin Hausawa sune Daurawa da suka bunkasa sai suka janyo hankalin mutane da dama daga mabanbantan wurare ciki harda Larabawa”, in ji farfesa Mahadi Adamu.
To masu salon Magana kan ce zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai, ko da al’adunsu suka fara cudanya sai kuma sabbin matsaloli suka bijiro, da suka hadar da yunwa da kuma yake-yake, a nan ne wasunsu suka fara hijira suna kafa wasu garuruwan da kuma sarautunsu, duk inda suka kafa gari sai su nada sarautarsu, da dama suna alakanta sarautarsu da ita Daura, amma wasu ba su alakanta ba.
LABARIN BAKA NA BAYAJIDDA
Wannan labarin baka na Bayajidda ya nuna cewa tarihin asalin Hausawa ya samo asali ne daga wani mutumi mai suna Abu-Yazidu wanda aka fi sani da Bayajidda. Labarin ya nuna cewa shi Bayajidda ya kasance dan Sarkin Bagadaza. An ce Bayajidda yayi rigima da mahaifin sa ne wanda ya sa dole yayi hijra zuwa yamma tare da wasu daga cikin mabiyan sa.
Kafin zuwan Bayajidda kasar Hausa, sai da ya sauka kasar Borno inda ya auri yar sarkin Bornon mai suna Magira. Sai dai daga Sarkin Borno ya nemi ya hallaka shi, don haka ya taho tare da Magira. Da suka zo wani gari mai suna Garun-Gabas sai matar sa Magira ta haihu, don haka ya bar ta anan ya kara gaba. Daga karshe, Bayajidda ya sauka a Daura inda ya nuna bajinta na kashe wata macijiya wadda ta addabi al’ummar garin. Saboda wannan bajintar, yasa Sarauniyar Daura mai suna Daurama ta aure shi. An ce sun haifi da Mai suna Bawo wanda shi kuma ya haifi yaya guda shida wadanda suka kafa Masarautun kasar Hausa wadanda ake kira da Hausa Bakwai kamar haka :
1, Bagauda a Kano
2, Kumayo a Katsina
3, Gunguma a Zazzau
4, Uban Doma a Gobir
5, Gazori a Daura
6, Zaman Kogo a Rano
7, Zauna Gari a Birom (Garun-Gabas)
Sai dai Kuma manyan masana Tarihin Asalin Hausawa sun bayyana labarin Bayajidda a matsayin tatsuniya. Misali, manazartan sun tabayi cewa shin mutanen da Bayajidda ya tarar a Daura wane harshe suke amfani da shi ?. Daga karshe manazartan sun ce labarin Bayajidda zai iya samun gindin zama da karbuwa ne kawai a matsayin Tarihin kafa Masarautun kasar Hausa.
✍️Saliadeen Sicey – 2022.