Rashawa: An Sauyawa Shari’ar Ganduje Kotu
Alƙaliyar Alƙalai ta jihar Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta sauya wa shari’ar da ake wa tsohon Gwamnan jihar, kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa a yanzu, Abdullahi Umar Ganduje, tare da ƙarin wasu mutane bakwai Kotu.
Shari’ar wacce ke gaban Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 4, da ke Sakateriyar Audu Baƙo, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Usman Malam Na’abba, ta samu sauyi ne zuwa Kotu mai lamba 7, da ke Miller Road, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Adamu.
Da ya ke tabbatar da cigaban, a ranar Alhamis, Kakakin Kotunan jihar Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya ce “Ofishin Alƙaliyar Alƙalai ya na da ikon sauyawa kowacce shari’a Kotu, a kowanne mataki ake a shari’ar, muddin dai ba a kai ga matakin yanke hukunci ba”.
Gwamnatin jihar Kano ce dai, ta gurfanar da Abdullahi Umar Ganduje, tare da Matarsa, da Ɗansa, harma da ƙarin wasu mutane, bisa tuhume-tuhume guda takwas, da ke da alaƙa da cin hanci da rashawa na biliyoyin Nairori.
Ba ya ga Ganduje da Iyalansa, sauran waɗanda su ke cikin ƙunshin shari’ar su ne: Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Ltd, Safari Textiles Ltd da Lesage General Enterprises.
A lokacin da Kotun ta ɗage cigaba da sauraron shari’ar a ranar 29 ga watan Afrilun da ya gabata kuma, ta tsara yanke hukunci ne a yau, sai dai gaza gabatar da sammaci ga waɗanda ake ƙara ya kawowa wannan yunƙuri cikas.