Labarai

Rashin Wutar Lantarki Ya Kawo Cikas Ga Zaman Majalissar Dattijai

Rashin wutar lantarki a Majalissar Dattijai ta ƙasa, ya jawo jinkirta zaman ƴan majalissar a ranar Talata, sakamakon jiran kawo wutar lantarkin da su ka yi, kafin fara zaman nasu na yau.

Wani faifan bidiyo da ke cigaba da karaɗe kafafen sada zumunta, ya nuna yadda majalissar ta ƙume da duhu.

A cewar gidan talabijin na Channels kuma, shugaban majalissar ta dattaijai, Godswill Akpabio, ya jagoranci fara zaman majalissar mintuna kaɗan bayan dawowar hasken lantarkin.

A jawabinsa kuma, ya haƙurƙurtar da membobi, tare da sauran mahalarta majalissar kan duhu da zafin da aka fuskanta a majalissar, ya kuma ƙara da cewar, har kawo yanzu akwai ofisoshin majalissar guda tara da ke cikin duhu, sai dai ana cigaba da aiki dan shawo kan lamarin.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button