Zamantakewa

Riƙo Da Al’adu Zai Taka Gagarumar Rawa Wajen Daƙile Rashawa – EFCC

Shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana watsi da nagartattun aládun da alúmmar kasar nan ke yi, a matsayin babban abin da ke kara taázzara rashawa.

Olukoyede, ya bayyana hakan ne jiya, ya yin da Shugaban Cibiyar Wayar Da Jamaá kan aládu, Biodun Ajiboye, ya kai masa ziyara, tare da tattauna batun hada kai domin cigaba da wayar da kan alúmmar kasar nan game da aládu, da ma bukatar da ke akwai ta sake farfado da su, domin yakar rashawa a kasar nan.

Ajiboye, ya ce hukumar na yin iya bakin kokarinta wajen kakkabe laifukan rashawa, kuma hanya guda ta cimma wannan nasara, ita ce ta wayar da kan yan kasa kan tasirin da aládu ke da su wajen inganta tarbiyya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button