Kasuwanci

Rikici Ya Ɓarke Tsakanin Dangote Da BUA

Shekaru biyu, bayan da tsohon Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci sulhunta fitattun ƴan kasuwar Kano, Alhaji Aliko Dangote, da Alhaji Abdul-Samad Isyaka Rabi’u (BUA), rikicin da ke tsakaninsu ya sake dawowa sabo.

Sai dai, rahotanni sun bayyana yadda dattijon attajiran nan, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ke ta kaiwa gwauro ya na kaiwa mari wajen ganin an samu fahimtar juna a tsakanin shahararrun ƴan kasuwar na Najeriya ƴan asalin jihar Kano.

Irin rawar da ƴan kasuwar ke takawa fage daban-daban, tare da kayayyakin da kamfanoninsu ke sarrafa abu ne da ke ƙara ɗaga kimar Najeriya, a idon ƙasashen duniya, tare da haɓɓaka cigaban ƙasar.

Sai rahotanni sun bayyana yadda tsohon rikicin da ke tsakanin ƴan kasuwar guda biyu, ya sake dawowa sabo a ƴan kwanakin nan.

Rukunin kamfanonin Dangote, sun zargi kamfanin BUA da ɓata musu suna, ta hanyar kushe kayayyakinsu ga abokanan kasuwanci, wanda hakan ke zama barazana ga cigaba da gudanar da kasuwancinsu.

Zargin na kamfanin Dangote kuma, ya fito ne ta cikin wani jawabi da kamfanin ya fitar, tun a ranar 2 ga watan Nuwamban da mu ke ciki, inda kamfanin ya musanta batun bincikarsa da aka ce ana yi, kan canzar da kuɗaɗen ƙetare ba bisa ƙa’ida ba, da ma hannun kamfanin cikin badaƙalar Dalar Amurka biliyan 3.4 da aka yi, tun a lokacin tsohon Gwamnan Babban Bankin Ƙasa, Godwin Emefiele.

Inda kamfanin ya bayyana rahoton a matsayin ƙagen da BUA ya yi masa, kamar yadda irin hakan ta taɓa kasancewa tun a shekarar 2016.

Da ya ke martani, ta cikin wani jawabi da kamfaninsa ya fitar, a ranar Juma’a, BUA ya bayyana yadda tun tsawon shekaru 32 da su ka gabata aka zargi Kamfanin na Dangote da aikata almundahana fagen kasuwancinsu daban-daban.

Ka zalika, BUA ɗin ya ce, ko a shekarar 1991 lokacin da aka fuskanci matsalar ƙarancin sukari a ƙasar nan, aka kuma yi sa’a kamfanin na BUA na da shi, ya kuma yi ƙoƙarin wadata ƙasar da shi ma, sai da kamfanin Dangoten ya nufe su da nufin shi ma ya saya, amma daga bisani matsaloli su ka shiga ciki, bayan da kamfanin ya bada takardar cakin kuɗin da bankin Societe Generale Bank su ka ƙi karɓa. Wanda har ta kai ga zuwa Kotu, inda Kotun ta garƙame wasu daga cikin kadarorimu – A cewar jawabin na kamfanin BUA.

“Bayan shekaru kaɗan kuma mu ka yanke shawarar samar da kamfanin Suga. Mu ka je wurin Marigayi Usman Dantata, wanda Kawun Dangote ne domin sayen fili mai girman kadada 4.5, mu ka sanya hannu kan yarjejeniya mu ka biya kuɗi, amma sai da Dangote ya bari mu na shirin fara aiki sai ya garzaya wurin tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya sa aka ƙwace wurin, aka mallaka masa. Wanda hakan ya sa har kawun nasa ma ya rasa wurin. Sa’o’i 24 kawai aka bawa BUA domin ya tattara komatsansa ya bar wurin.

“Dan haka bai zama lalle a shawo kan lamarin nan yanzu ba.”, a cewar jawabin.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button