Kotu

Rikicin Fili : An Maka Zaɓaɓɓen Ɗan Majalissa, A Gaban Kotu

Mutane huɗu dai, aka gurfanar a gaban babbar kotun Upper Area, kan wannan rikici, ciki kuwa har da zaɓaɓɓen ɗan majalissa, mai wakiltar Keffi ta Yamma, a majalisar jihar Nasarawa, Baba Ali Nana.

Rikicin filin wanda ke garin Mararaban Gurku dai, a yanzu ya kasance guda daga cikin manyan batutuwan da ake tattaunawa, bayan da aka gudanar da zaman kotu, a ranar Litinin, 15 ga watan Mayun 2023.

Kuma alƙali ya buƙaci a kai takardar sammaci wajen mutum na 3 da ake ƙara, kamar yadda Barista Isa Hassan Nalaraba ya bayyana wa Wakilin jaridar ATP cewa, a halin yanzu kotun ta sanya ranar 31 ga wannan wata na Mayu domin cigaban Shari’ar.

An samu tsaikon cigaba da sauraren ƙarar da Alhaji Sani Ahmad Zangina ya shigar da Shugaban Kasuwar ta Ƴan lemu kan filin, wanda ke maƙwabtaka da kasuwarsu ta ƴan lemo a gaban kotun ne dai, bayan samun rahoton gaza isar takardar sammaci ga ɗaya daga cikin mutanen da ake ƙara.

Wanda hakan ne ya tilasta Alƙali ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 31 ga wannan wata na Mayu, a matsayin ranar da za’a cigaba da sauraren ƙarar.

A gefe guda kuma, wakilinmu ya tuntuɓi Lauyan wanda ake ƙara, Barista Chinedu wanda shine Lauyan ɗan majalisa mai wakiltar shiyyar Keffi ta yamma Baba Ali Nana.

A ya yin da ake cikin kotu dai, Lauyan wanda ake ƙara ya roƙi kotu da ta yi afuwa, bisa rashin zuwan ɗan majalisar akan lokaci, inda kafin haka Lauyan mai ƙara Isa Hassan, ya bukaci a kamo ɗan majalisar, saboda rashin halartan kotun, wanda rashin martaba ta ne, duba da cewa sammacin kotun ya isa hannunsa.

Sai dai kafin kotun ta bayyana matsayarta, kan bada umarnin kamo ɗan majalisar, sai aka hangi Ɗan Majalisar ya shigo kotu a gaggauce, inda kotun tace, babu buƙatar gabatar da wannan roƙo, tunda ɗan majalissar ya samu halarta.

Wani abin da yafi ɗaukar hankalin masu sauraron Shari’ar dai, shi ne yadda Ɗan Majalisar ya gaji da tsayuwa, ya kuma zauna ba tare da izinin kotu ba, amma lauyan mai ƙara Nalaraba ya ankarar da kotun, inda kuma nan take kotu ta nemi Ɗan Majalisar ya tashi tsaye domin sauraron yadda zata kaya, kan buƙatar bayar da Belinsa, da lauyansa ya ke nema.

Inda daga bisani kotun ta sahale masa ya zauna, sakamakon lura da halin da ya shiga na takura.

Credit : ATP Hausa

Edited : Rariya Online

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button