Kimiyya Da Fasaha

Rundunar Ƴan Sanda Ta Ƙaddamar Da Banɗakin ‘Tafi Da Gidanka’

Sufeto Janar ɗin rundunar ƴan sandan ƙasar nan, na riƙon ƙwarya, Kayode Egbetokun, ya ƙaddamar da wasu kayayyakin tafi da gidanka (Mobile) da rundunar ta samar a Kwalejin Horas da Jami’an Ƴan Sanda ta Ikejan jihar Legas, a ranar Juma’a.

A cewar sa dai, kayayyakin za su taka muhimmiyar rawa wajen bawa Jami’an Ƴan Sandan damar daƙile matsalolin tsaro a jihar, tare da kawo ƙarshen matsalar ƙarancin muhalli, a makarantar.

Kayayyakin da aka ƙaddamar sun haɗarda, Banɗaki, Ɗakunan wanka, Ɗakin Girki, da makamantansu.

Ya kuma ƙara da cewar, rundunar ƴan sanda na shirya wata tawaga ta musamman da za ta yi Aikin kakkaɓe ayyukan ta’addanci a ƙasar nan.

Bugu da ƙari kuma, za a aike da Jami’an tawagar ne zuwa kowacce jiha da ke faɗin ƙasar nan.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button