Rundunar Ƴan Sanda, Ta Jadda Matakin Haramta Tuƙin Adai-daita Sahu, A Kano
Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta bayyana cewar, har yanzu dokar nan ta haramta zirga-zirgar baburan adai-daita sahu, a jihar, daga ƙarfe 10 na dare, zuwa 6 na safe, na nan daram, inda ta buƙaci matuƙa baburan da su cigaba da kasancewa masu biyayya ga dokar.
Ka zalika, rundunar ta kuma sake bayyana haramcin yin kilisa da Dawakai, a ƙwaryar birnin jihar, musamman a wannan wata mai Alfarma, na Ramadan, da mu ke ciki.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne ya bayyana hakan, ga manema labarai, a birnin Kano.
”Rundunarmu, za ta haɗa hannu da sauran rundunonin tsaro, da ma hukumar kula da zirga-zirga, wajen ganin an kama dukkannin masu karya wannan doka.
”Ka zalika, ita ma Kilisa, da harba Knock-Out an haramta su, kuma za a kama dukkannin masu take wannan doka” A cewar Kiyawa.