Rundunar Ƴan Sandan Kano Ta Kama Ɓarayin Ababen Hawa 15
Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta ce, ta kama kimanin mutane 15 da ake zargi da satar ababen hawa, tare da ƙwato motoci 20 da aka sace a sassan jihar.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Talata , a birnin Kano.
Ya ce wannan nasarar ta samo asali ne daga ƙudurin rundunar na kawo ƙarshen duk wasu laifuka a jihar.
Kiyawa ya ce, sun himmatu sosai wajen yaƙar satar motoci da duk wasu nau’oín aika-aika a wuraren da suke sa ido.
A watan da ya gabata ne dai, rundunar ƴan sandan ta sanar da ninka jajircewarta, domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin ɗaukacin mazauna jihar.
Kazalika Kiyawa ya miƙa godiyarsa ga jama’ar jihar, kan haɗin kai da goyon bayan da ake ba su.