Rundunar Ƴan Sandan Kano Ta Kama Ɗan Sandan Da Ya Harbe Wani Mutum A Kurna
Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta kama-tare da tsare, Jami’in Ɗan Sandan, da ake zargi da harbin mutane, a unguwar Kurna, inda mutum guda ya rasa ransa.
Bayanin hakan, na ɗauke ta cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ta shafinsa na kafar sada zumunta, a yau Laraba.
Lamarin dai, ya faru ne a unguwar Kurna, da ke ƙaramar hukumar Fagge, a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamban 2023, bayan da wasu gungun matasa su ka kama faɗa, wanda hakan ne ya sanya wancan Jami’in Ɗan Sanda, yin harbinda ya raunata mutane biyu, tare da rasuwar mutum guda, ya yin da ya ke karɓar kulawa a Asibiti.
Sai dai, tuni Kwamishinan Ƴan Sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel, ya bawa Kwamandan rundunar na Dala, ACP Nuhu Mohammed Digi, umarnin bincikar lamarin.
Daga bisani kuma, an kama Jami’in bisa tuhumarsa da aikata laifin kisan kai.