Siyasa

Saƙon Taya Murnar Samun Nasara A Kotun Ɗaukaka Ƙara Ga Gwamnan Nasarawa, Daga Alhaji Sani Ahmad Zangina

Shugaban rukunin kamfanonin Jaridun yanar gizo na Rariya Online da Karamchi, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya aike da saƙon taya murnar samun nasara a Kotun ɗaukaka ƙara, ga Gwamnan Nasarawa, Abdullahi A. Sule.

Saƙon taya murnar, wanda fitaccen Ɗan Jaridar ya ɗauka ta sigar hoto mai motsi (bidiyo) tare da wallafawa a shafukansa na sada zumunta na zamani, da ma wasu shafukan jaridu, ya ƙunshi yabo da jinjina ga Kwamishinan Shari’a na jihar ta Nasarawa, Barista Labaran Magaji, kan irin gagarumar rawar da ya taka, wajen tabbatar da samun wannan nasara.

Ka zalika, ya ƙara da fatan cigaba da sharɓar romon Demokraɗiyya ga talakawan jihar, kamar yadda su ka amfana a zangon mulkinsa na farko.

Alhaji Sani Ahmad Zangina, guda ne daga cikin al’ummar jihar da ke matuƙar nuna goyon baya ga Siyasar Gwamnan na APC, wanda kuma ke zaune a ƙaramar hukumar Karu.

Idan ba a manta ba dai, a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne, Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da Gwamna Abdullahi A. Sule na jam’iyyar APC, a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan jihar, bayan da ta yi watsi da hukuncin Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar ta Nasarawa, wanda ya bawa ɗan takarar PDP nasara.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button