Rahotanni

Saɓanin Fahimta Ya Kaure Tsakanin Lauyoyin Rarara Da Alhaji Sani

Saɓanin fahimta ya kaure tsakanin Lauyoyin ɓangarorin Mai Ƙara, Da na wanda ake ƙara, a shari’ar da fitaccen Ɗan Jaridar nan, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya shigar da Mawaƙin Siyasa Dauda Kahutu Rarara, a gaban Babbar Kotun Majistiri, mai lamba ɗaya, da ke jihar Nasarawa, bisa zarginsa da furta kalaman da ka iya jawo tunzuri a tsakanin al’umma, ya yin wani taron Manema Labarai, da ya gudanar, cikin shekarar da ta gabata, a jihar Kano.

A ya yin zaman da Kotun ta gudanar, da safiyar yau (Juma’a), 2 ga watan Fabrairun 2024 dai, ba a hangi fuskar Mawaƙi Rarara a gaban Kotun ba, duk kuwa da umarnin da Kotun ta bayar na neman bayyanarsa a gabanta, ya yin zaman ƙarshe na shari’ar da ya gudana, tun a ranar 8 ga watan Janairu.

Ko da muka miƙa abin magana ga guda cikin Lauyoyin Mawaƙin kuma, sai ya bayyana mana cewar, Rararan bai bayyana a gaban Kotun bane, sakamakon ƙarar da ya ɗaukaka a gaban Babbar Kotun jihar ta Nasarawa, da ke Doma, kan umarnin Kotun Majistirin na buƙatar ya bayyana a gabanta, ya yin zaman na yau.

Cikin buƙatun da Rararan ya shigarwa babbar Kotun kuma, har da neman dakatar da shari’ar da Kotun Majistirin ke saurara akansa, har sai Babbar Kotun jihar ta bayyana matsayarta kan ƙarar da ya ɗaukaka, na rashin buƙatar bayyanarsa a Kotun, duba da yadda tun a karon farko Lauyoyinsa, su ka bayyanawa Kotun cewa, ba ta da hurumin sauraron shari’ar ma baki ɗaya, amma ta ƙeƙasa ƙasa, tace dole ya bayyana, domin amsa aikata laifin ko rashinsa, kafin duba batun hurumin sauraron ƙarar, ko akasin haka.

Duk da amincewa da ɗaukaka ƙarar da Rararan ya yi daga Babbar Kotun jihar, tare da ranar 12 ga watan Fabrairun da mu ke ciki, da Kotun ta sanya domin dukkannin ɓangarorin su bayyana a gabanta, domin sauraron matsayarta game da batun, Lauyan Mai Ƙara, Barista Nalaraba ya ce, akwai sauran Rina a kaba, domin kuwa sun roki Kotun Majistirin da ta sanya ranar 9 ga watan Fabrairun da mu ke ciki, a matsayin ranar komawa domin cigaba da shari’ar, duba da cewar, dukkannin ɗaukaka ƙarar da wani ɓangare ya shigar ba tare da sanin ɗaya ɓangaren ba, wa’adinta ya kan kawo ƙarshe ne, bayan kwanaki bakwai, wanda kuma wa’adin zai kare ne, kafin waccar ranar ta 12 ga Fabrairun da babbar Kotun ta sanya.

Sharshin Jaridar Rariya, baya wuce kalmar nan ta ƴan Hausa, wato “Ga Fili ga mai doki”, za kuma mu tara a waccar rana ta 9 ga wata, dan rawaito muku yadda lamarin zai kasance.

Miftahu Ahmad Panda, daga Kotun Majistirin jihar Nasarawa, a Jaridar Rariya Online.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button