Rahotanni

Sai An Fara Aiki Dan Kishin Ƙasa, Kafin Najeriya Ta Gyaru – Alhaji Sani

Fitaccen Ɗan Jaridar nan, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya bayyana cewar, Najeriya za ta gyaru ne ta hanya ɗaya tilo, lokacin da dalilin yin aiki zai zamo ganin dama, da kuma Kishin Ƙasa, bawai kawai dan neman mafita, kamar yadda ake gani a halin yanzu ba.

Zangina, ya bayyana hakan ne, cikin wani saƙo da ya wallafa, ta shafinsa na kafar sada zumunta ta Facebook, da yammacin Alhamis, 21 ga watan Maris.

“Hanyar dana hango ta gyaran Najeriya daya tilo ita ce lokacin da aiki zai zamo ganin dama da kuma kishin kasa a matsayin dalil bawai neman mafita ba.”, a cewarsa.

Ta cikin wani saƙo na daban, da ya wallafa a harshen Ingilishi kuma, Ɗan Jaridar ya bayyana ayyukan Ƴan Sanda, da na Soji, tare da sauran hukumomin tsaro, a matsayin misalin ire-iren ayyukan da ake fatan Kishin Ƙasar ya tsunduma al’umma a ciki.

Ba sabon abu bane ba dai, yadda ake ganin ƴan Najeriya na shiga ayyuka daban-daban, da nufin wawurar dukiyar tserewa talauci, wanda hakan ke cigaba da zamowa ɗan zani ga cigaban Najeriyar.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button