Ilimi

SAMA DA ƊALIBAI DUBU GOMA NE, KE CIKIN BARAZANAR RASA GURABEN KARATU, A MANYAN MAKARANTUN ƘASAR NAN

Hukumar JAMB ta jaddada cewar, ba za ta bada guraben karatu (Admissions) ga Ɗaliban da ke neman shiga Jami’a kaitsaye (DE) ba, muddin sun fito ne, daga guda cikin makarantun da ta wallafa a jadawalinta mako-mako (JAMB Bulletin) ba.

Hakan kuma, na faruwa ne, sakamakon gaza amincewar makarantun da sabon tsarin da hukumar JAMB ta ɓullo da shi, a shekarar 2023, na tantance sakamakon kammala karatun A’Level ɗin Ɗalibai, kafin basu guraben karatu, a Jami’o’i, bayan da ta zargi da dama daga cikin Ɗalibai da yin amfani da sakamakon kammala makarantun gaba da Sakandire na bogi, wajen neman guraben karatu a Jami’o’in ƙasar nan.

Kimanin makarantu 245 ne kuma ke cikin wannan rukuni na non-responsibe, wanda hakan ke zama barazana ga ɗaukacin ɗaliban da su ka fito daga makarantun.

Dukkannin sakamakon da aka tantance a ƙarƙashin sabon tsarin na Certificate Verification dai, ya na shiga rumbun da hukumar JAMB ta samar na tattara sakamako ne, mai suna NIPEDS.

Tsarin na Certificate Verification kuma, ya fara ne daga shekarar 2023, wanda hakan ke tabbatar da cewar, dukkannin ɗaliban da makarantunsu ke cikin non-responsibe, to ba za su samu guraben karatu ba, tun daga shekarar 2023 har abin da hali ya yi.

Sama da Ɗalibai 10,378 ne kuma, wannan lamari zai shafa.

Domin Tambaya – 08039411956

✍️ Miftahu Ahmad Panda.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button