Sama Da Biliyan Uku Gwamnatin Kano Za Ta Kashe Wajen Ɗaukar Nauyin Karatun Ɗalibai A Ƙasashen Ƙetare
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewar, ta na da shirin kashe sama da Naira biliyan 3 da rabi, wajen biyan kuɗaɗen tallafin karatun ƙasashen ƙetare, ga ɗaliban Jihar kimanin 550 da Gwamnatin za ta ɗauki nauyin karatunsu na Digiri na biyu, da na Uku.
Kwamishinan Ilimi mai zurfi na jihar, Dr. Yusuf Ƙofar Mata, shi ne ya bayyana hakan, ranar Juma’a, a birnin Kano, ya yin da ya ke zantawa da Manema Labarai, bayan kammala zaman Majalissar zartarwa na mako-mako.
Inda Kwamishinan ya ce, Ɗaliban za su yi karatu ne, a Jami’o’in ƙetare guda bakwai, da ke ƙasashen India da Uganda.
Ya kuma ce, an zaɓi Ɗaliban kimanin 550 ne, daga cikin guda 1,250 da su ka nuna sha’awarsu ta samun wannan tallafin karatu.
Ka zalika, ya ƙara da cewar, an bada dama iri guda ne ga dukkannin ɗaliban, ba tare da duba banbancin ra’ayin Siyasa ba, muddin dai Ɗaliban sun kasance ƴan asalin Jihar Kano, kuma sun cancanta.
Bugu da ƙari, Dr. Ƙofar Mata ya ce, tuni Gwamnati ta kammala samar da takardun izinin shiga ƙasa (VISAS) ga ɗaliban waɗanda za su tafi zuwa makarantunsu a ƙarshen wannan watan.
“Mun karɓi saƙonnin nuna buƙata (Applications) daga ɗalibai 1,250 da ke da sha’awar yin karatun Digiri na Biyu da na Uku, kuma mun tantance su, inda a ƙarshe muka samu 550 ƴan asalin Jihar Kano da su ka cancanta, waɗanda kuma Gwamnati za ta ɗauki nauyin karatunsu a Jami’o’in ƙetare.
“A yanzu haka kuma muna tattara dukkannin takardu da bayanan da ake buƙata daga ɗaliban ne, domin shirye-shiryen Visa.
“Muna fatan zuwa ƙarshen watan nan, waɗannan ɗalibai za su fara tafiya zuwa Jami’o’in da su ka samu guraben karatu, domin fara karance-karancensu, a fannoni mabanbanta”.