Kotu

Sama Da Kaso 90 Na Sanatocin Najeriya, Su Na Fuskantar Shari’o’i A Gaban Kotu

Ƴar Majalissar Dattijai, da ke wakiltar babban birnin tarayya Abuja, Ireti Kingibe, ta bayyana cewar, sama da kaso 90 na Sanatocin Majalissar ƙasar nan ta 10, su na fuskantar shari’o’in zaɓe a gaban Kotuna daban-daban.

Kingibe, ta bayyana hakan ne, ya yin wani taron Manema Labarai, da ta gudanar ranar Laraba, a babban birnin tarayya Abuja, inda ta ce hankalin ɗaukacin Sanatocin ya na kan shari’o’in babban zaɓen 2023.

Sanatar ta Jam’iyyar LP, ta bayyana waɗannan kalamai ne kwana guda, bayan da Kotun sauraron shari’un zaɓen Sanatoci, ta sake tabbatar da ita a matsayin halastacciyar Sanatar da ke wakiltar babban birnin tarayya Abuja, a ranar Talata.

Majalissar Dattijan ƙasar nan dai, na da membobi kimanin 109.

“A makonni takwas da su ka gabata, ko wani lokaci mai kama da hakan, sama da kaso 90 na Sanatoci hankalinsu ya na Kotuna wurin shari’un zaɓe, ko wasu Shari’o’in na daban. Ina so ƴan Najeriya su bamu lokaci, dan ganin me za mu iya kaiwa Majalissar. Za ku iya ganin rawar da zamu taka cikin makonni takwas.

“Amma zuwa yanzu mun dawo hayyacinmu, kuma ƙararrakin zaɓen da su ka ɗauke mana hankali a Kotuna, sun ƙare yanzu, da zarar mun kammala warwarewa, Jama’ar Najeriya za su ga yadda Sanatoci za su gudanar da Ayyukansu cikin mayar da hankali, da kishin yankuna, da ƙasa”, a cewarta.

Sanata Kingibe, ta kuma yi kira ga Abokan burminta na Siyasa da su zo su haɗa hannu, dan ganin an haɓɓaka babban birnin na tarayya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button