Sama Da Mazauna Gaza 300,000 Ne Ke Rayuwa Cikin Yunwa
Hukumomin Majalissar Dinkin Duniya sun yi gargadi kan matsalar karancin abinci da yunwa da su ka mamaye yankin Gaza, tare da raba dubban mutane da muhallansu da luguden wutar Isra’ila ya haifar, ya yin da samun abincin sanyawa a bakin salati ya gagari dai-daikun da su ka rage.
Ta cikin wani jawabin hadin guiwa da Sashen kula da yalwar abinci, da ma UNICEF, da hukumar lafiya ta duniya su ka fitar, sun bayyana cewar, wajibi ne a bude hanyar zirin na Gaza, domin samun damar isar da kayayyakin agaji.
Duk kuma da cewar kaitsaye Majalissar dinkin duniya ba ta dora alhakin dakile damar shiga Gaza din ga Isra’ila ba, hukumomin sun ce ba a barin wadatattun motocin dakon kaya su tsallake cibiyar binciken kan iyakar kasar, a kowacce rana.
Inda su ka yi kira da a saurarawa ma’aikatan da ke kai kayayyakin agajin ta fuskar basu damar gudanar da zirga-zirga a yankin, dan tabbatar da isar kayan agajin ga masu rabawa, da wadanda za su amfana.
Yanzu haka dai, akwai kusan mutane 300,000 da ke rayuwa a yankin na Gaza, duk kuwa da rushewar gidajen da ake cigaba da fuskanta, sakamakon azabtarwar Isra’ila.