Tsaro

Sama Da Mutane 67 Aka Nema Aka Rasa A Jihar Gombe

Aƙalla mutane 67 aka kai rahoton ɓacewarsu, ga rundunar ƴan sandan jihar Gombe, cikin watanni tara.

Da ya ke tabbatar da hakan, a ya yin zantawarsa da Jaridar PUNCH, ranar Talata, Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Mahid Abubakar, ya ce an kai rahotannin ɓacewar mutanen ne, daga ƙananan hukumomi 11 da ke Jihar. Mutum 65 ne dai aka bayyana ɓacewarsu, ya yin da 2 kuma ake kan tuntuɓa, wanda ya kai jimillarsu zuwa 67.

Abubakar, ya kuma ce, an samu waɗannan rahotanni ne, daga watan Janairu, zuwa Satumban 2023.

Ya kuma ce, mafi yawa Iyalan waɗanda aka rasa ɗin ne, su ke shigar da ƙorafi ga hukumar ƴan sanda.

A ƙarshe, ya tabbatarwa da Mazauna jihar ta Gombe cewar, Kwamishinan ƴan sandan jihar, Oqua Etim, tare da Jami’ansa, na yin iya bakin ƙoƙarinsu, wajen ganin sun samar da tsaro, ga al’ummar Jihar, “Dan haka babu buƙatar fargaba” a cewarsa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button