Ilimi
Sanarwa Ga Ɗaliban Da Ke Neman Kano State College Of Nursing
Kwalejin Nazarin Harkokin Lafiya (Kano State College Of Nursing), na kira ga dukkannin ɗaliban da su ka nemi Makarantar, su ka biya kuɗi, tare da sanya sakamakon kammala Makarantar Sakandire, da sauran takardunsu a shafinta, amma har yanzu ba su samu Application Slip ɗinsu, da ke ɗauke da Application Number (Ba tmp Number ba) cewar, akwai buƙatar su halarci sashen kula da Al’amuran Intanet, da Adana bayanai na makarantar, ɗauke da Original, da Photocopy na Takardunsu, daga ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba, zuwa ranar Talata, 26 ga watan na Satumbar 2023 da mu ke ciki.
Akwai buƙatar dai, Ɗalibai su hanzarta yin amfani da wannan dama, ya yin da ya rage kwanaki 5 kacal.