Sanarwa Ta Musamman Ga Malaman BESDA, Na Jihar Kano
Wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 01 ga watan Disamba, da Abba Rabiu Gwarzo, ya fitar, a madadin Kwamishinan Ilimi na jihar Kano, ta buƙaci ɗaukacin Malaman BESDA, da su halarci cibiyoyin da aka tanada a ƙananan hukumomin su, a gobe Asabar, 02 ga watan Disamban 2023, domin rubuta jarrabawar ɗaukarsu aiki.
A cewar sanarwar dai, hakan shi ne zai tabbatar da ɗaukar ma’aikatan ta sahihiyar hanya, tare da tabbatar da sahihancinsu, bayan kammala tantancesu.
Za kuma, a rubuta jarrabawar ne, a ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar, guda 44, da misalin ƙarfe 8:30 na safiya.
GA JERIN SUNAYEN CIBIYOYIN DA ZA A RUBUTA JARRABAWAR, A KOWACCE ƘARAMAR HUKUMA :
1. Ajingi: Ajingi Model Primary School.
2. Albasu: Panda Central Primary School.
3. Bagwai: Government Girls Junior Secondary School Bagwai.
4. Bebeji: Bebeji Coexist.
5. Bichi: Sabon layi Primary School.
6. Bunkure: Bunkure Central Primary School.
7. Dala: Goverment Secondary School Dala, Gwammaja 1.
8. Dambatta: Dambatta Model PS.
9. D/Kudu: D/Kudu Model PS.
10. D/Tofa: D/tofa SPS.
11. Doguwa: Tsagwayam focus PS.
12. Fagge: Fagge Model PS.
13. Gabasawa: Zakirai Model PS.
14. Garko: Garko CFSI.
15.G/Malam: Ciromawa idi SPS.
16. Gaya: Dagara CFSI.
17. Gezawa: Shehu Ringim Science.
18. Gwale: Dukawuya Girls Project.
19. Gwarzo: Gwarzo Model PS.
20. Kabo: GJSS late Dankabo.
21. KMC: Shahuci SPS.
22. Karaye: Chedi Model PS.
23. Kibiya: kibiya Yamma PS.
24. Kiru: Kogo PS.
25. Kumbotso: Panshekara SPS.
26. Kunchi: CAS Kunchi annex.
27. Kura: Danshado ibadi Islamiyya.
28. Madobi: Kafin Agur Model PS.
29. Makoda: Koguna CPS.
30. Minjibir: Boarding PS.
31. Nasarawa: Gwagwarwa PS.
32. Rano: Abubakar Ila SPS.
33. R/Gado: R/gado SPS.
34. Rogo: Ruma PS.
35. Shanono: Child friendly Initiative.
36. Sumaila: Sumaila Gabas SPS.
37. Takai: Takai SPS.
38. Tarauni: U/uku Model PS.
39. Tofa: Doka SPS.
40. Tsanyawa: Tsanyawa SPS.
41. T/Wada: GGSS Coexist K/Ikara.
42. Ungogo: Bachirawa SPS.
43. Warawa: Upper Basic Coexist.
44. Wudil: KUST Staff School.
Allah ya bada nasara.