Labarai
Sanata Ahmad Wadada Ya Ƙaddamar Da Rabon Kayayyakin Sana’a Ga Al’ummar Yankinsa
A ranar Lahadin da ta gabata, 19 ga watan Nuwamban da mu ke ciki ne, Sanata Ahmad Aliyu Wadada, ya ƙaddamar da rabon kayayyakin sana’a ga al’ummar yankinsa.
Sanata Aliyu Wadada, wanda ke wakiltar gundumar Nasarawa ta yamma a Majalissar Dattijai ta ƙasa ya raba kayayyakin ne, ga ɗumbin Mata da Matasa, har ma da Magidanta da su ka fito daga shiyyar tasa.
Kayayakin da Sanatan ya raba, sun haɗarda Kekunan ɗinki, da Injinan Markaɗe.
Ta cikin wani saƙo da ya wallafa ta shafinsa na Facebook, Alhaji Sani Ahmad Zangina, wanda guda ne daga cikin al’ummar jihar ta Nasarawa, ya bayyana cewar, rabon da ƴan yankin na Nasarawa ta yamma su ga wani abu mai suna ‘Romon Dimokraɗiyya’ ya gifta, tun zamanin Sanata Abubakar Danso Sodangi.