Kasuwanci

Sanatoci Sun Amince Da Buƙatar Tinubu Ta Karɓo Bashin Dala Miliyan 500, Domin Sayen Mitoci

A ranar Larabar da ta gabata ne, Membobin Majalissar Dattijai ta ƙasa, su ka amince da buƙatar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aike musu ta sahale masa ya ranto Dalar Amurka Miliyan 500, domin samar da mitocin wutar lantarki a ƙasar nan.

Majalissar, ta amince da ciyo bashin ne, bayan karɓar rahoton kwamitin ta na Basussukan Cikin Gida da na Ƙetare, wanda Mataimakin shugaban Kwamitin, Sanata Haruna Manu (na Taraba ta tsakiya) ya gabatar.

Bashin na Dalar Amurka Miliyan 500 kuma, wani ɓangare ne na Dala biliyan 7.94 na basussukan bankin duniya, da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya samu sahalewar Majalissar domin karɓowa, tun a ranar 1 ga watan Nuwamban 2023.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button