Labarai
Sanatoci Sun Amince Da Dokar Tsawaita Shekarun Ma’aikatan Majalissa
Ƴan Majalissar Dattijai, sun amince da ƙudirin dokar tsawaita lokacin aikin ma’aikatan majalissar tarayya zuwa 65, daga shekaru 60 da su ke a baya.
Ƙudirin dokar, wanda tuni ya samu sahalewar majalissar wakilai, ya ƙara dacewa da sahalewar ƴan majalissun na Dattijai ne a ranar Alhamis, bayan gaza samun amincewa da ya yi a ranar 22 ga watan Fabrairu.
Jagoran Sanatocin, Bamidele Opeyemi, na jam’iyyar APC, daga jihar Ekiti, shi ne ya gabatar da Ƙudirin dokar, mai taken: “Ƙudirin Tsawaita Wa’adin Aikin Ma’aikatan Majalissar Tarayya”.
Bayan tafka muhawara kuma, ƙudirin ya samu sahalewar kaso mafi tsoka na membobin majalissar.
Najeriya dai, na da Majalissun tarayya guda biyu ne, da su ka haɗarda da: Majalissar Dattijai, da ta Wakilai.