Sanatoci Sun Fara Biyan Kuɗi Domin Samun Kujerar Shugabancin Majalissa – A Cewar Ali Ndume
Sanata Ali Ndume, da ke wakiltar Borno ta Kudu, a majalissar Dattijai, ya ce yadda ya ke da sanin makamar Aikin majalissar, zai iya shugabantarta, da a ce ya na da kuɗin da zai nemi shugabancin.
”Da a ce ni mai kuɗi ne, zan yi amfani da kuɗina wajen neman shugabancin majalissar Dattijai, kamar yadda ake yi a yanzu, tun da ina da ƙwarewa. Babu wani abu mai suna ‘duba cancanta’, komai yanzu ya zama na kuɗi. Hakan ne ya sanya har waɗanda basu san komai game da Aikin majalissa ba ma, su ke nuna sha’awar shugabantarta, kawai saboda su na da kuɗi”, a cewar sa.
Ndume, wanda ya bayyana hakan, a ya yin zantawarsa da sashen Hausa na BBC, a ranar Talata, ya ce tuni tsarin siyasar Najeriya ya zama wani iri, inda aka yi watsi da amfani da cancanta, domin kuwa kowanne ɗan Majalissa ya na iya amfani da kuɗinsa domin mallakar kujerar lamba ɗaya, a majalissar.