Sanyi: Gidauniyar Aminu Magashi Za Ta Tallafawa Hukumar Kashe Gobara, Ta Kano
Gidauniyar AMG, ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Aminu Magashi Garba, ta sha alwashin tallafawa Hukumar Kashe Gobara ta jihar Kano, wajen daƙile yawaitar tashin gobara a jihar.
Dakta Magashi, ya sanar da hakan ne, a ya yin wata ziyara da gidauniyar ta kaiwa Kwantirolan Hukumar kashe gobarar na jihar Kano, Engr. S.O. Kazeem.
Gidauniyar AMG dai, ta shafe tsawon shekaru ta na gudanar da ayyukan jin ƙai, da ba da tallafi wajen bunƙasa tsaro a yankin birni, da ƙauyen jihar Kano.
Ya yin da yanayin sanyi ke ƙara kankama, wanda hakan ke bayyana ƙaruwar haɗarin ɓarkewar gobara, sakamakon mu’amalar da mutane su ke yi da wuta kuwa, Gidauniyar ta bayyana aniyarta ta tallafawa hukumar kashe gobara ta Kano, da kayayyakin da ta ke buƙata, domin kiyaye rayuka da dukiyoyin alúmma.