Nishaɗi

Sarauniyar Kyawun Najeriya Ta Farko, Ta Cika Shekaru 93 A Duniya

Matar da ta lashe kyautar sarauniyar kyawun Najeriya ta farko, tun a shekarar 1957, Grace Oyelude, ta cika shekaru 93 da haihuwa, a yau (Alhamis).

Bayanin zagayowar ranar haihuwartata, ya fito ne, ta cikin wani saƙo da shafin Instagram na Miss Nigeria Organisation ya wallafa, a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba.

Inda saƙon ke cewa, “Muna masu farinciki, tare da taya murna ga Sarauniyar kyawu, kuma Jagorar Sarakunan Kyan Najeriya, Chief Grace Atinuke Oyelude, bisa cikarta shekaru 93 cif! da haihuwa.

“Ƙwarin guiwarta, ƙoƙarin samar da mafita, da ma ɗabi’arta ta jajircewa, su ne manyan nagartattun ɗabi’un da su ke ƙara mata kima a idonmu, da sauran al’umma.

“Muna ƙara taya murnar zagayowar ranar haihuwa, ga Sarauniyar kyawun Najeriya ta farko, Chief Grace Atinuke Oyelude.

“Muna yi miki godiya bisa share hanyar, tare da samar da kyakykyawan tsarin da dukkannin Sarakunan kyawun Najeriya su ke bi, da ma gudunmawarki ba tare da gajiyawa ba, wajen tabbatar da cigaban mata”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button