Sarkin Kano Ya Yaba wa Gwamnatin Ganduje
Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yaba wa namijin ƙoƙarin, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a tsawon shekaru takwas.
Sarkin ya bayyana haka ne, a ya yin ziyarar barka da sallah ya kai wa Gwamnan a jiya Lahadi.
Wata sanarwar da sakataren yaɗa labaran mataimakin Gwamna, Hassan Musa ya fitar, ta rawaito yadda mai martabar ke cewa; Ganduje ya samar, tare da gudanar manyan ayyukan da al’umma ke da buƙata a jihar Kano.
Ya kuma ƙara da cewa, jihar ta Kano ta samu kyakykyawan sauyi ta fuskar shugabanci, bisa haɗin guiwar Masaurata.
Sarkin ya kuma ƙara da yin kira ga Al’ummar jihar Kano, da su bada haɗin kai, domin samun nasarar gudanar da shirin ƙidaya na ƙasa da za a yi a farkon wata mai kamawa, na Mayu.
Haka zalika, Sarkin ya kuma bayyana farin cikinsa ga shugabancin Gwamna Ganduje, bisa rawar da ya taka, wajen tabbatar da shi a matsayin Magajin Kakanninsa, a masarautar Kano.
A nasa ɓangaren, Gwamna Ganduje, wanda ya samu wakicin mataimakinsa , Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, ya nuna jin daɗinsa bisa irin gudunmawar da ya ke samu daga masauratar ta Kano, musamman a fannin gudananr da shirye-shiryen da gwamnati ke bijirowa da su.