LabaraiUncategorized

Sau Huɗu Buhari Ya Ke Zuwa Gona A Kowanne Mako, Tun Bayan Saukarsa Daga Mulki

Garba Shehu, da ke zama mai magana da yawun tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewar, shugaban ya shafe dukkannin lokacinsa bayan barin Ofis ne, ya na halartar gonarsa, da ke garin Daura, a jihar Katsina.

Garba Shehun dai, ya ce, tsohon shugaban na halartar gonarsa sau huɗu, a kowanne mako guda.

Ya kuma bayyana hakan ne, ta cikin wani jawabi da ya fitar, a ranar Alhamis, mai taken ‘kwanaki 100 bayan Buhari’.

Jawabin ya ce, Buharin ya zaɓi zama a Daura ne, domin nisanta kansa da babban birnin tarayya Abuja, da zummar ƙauracewa tsoma baki kan al’amuran sabuwar Gwamnatin jam’iyyar APC, da ma samun isashshen hutu.

Ga dai abin da wani sashe daga jawabin ya ke cewa, “Ya na zuwa gona tsawon kwanaki huɗu a sati, kuma yadda amfanin gona da dabbobinsa su ka bunƙasa ya na da matuƙar ban sha’awa. Ya samu damar hutawa, amma ya ce sam ba zai bari ya yi mutuwar zuciya ba”.

Sanarwar ta kuma bayyana yadda tsohon shugaban ya ke cigaba da samun ziyara daga Ƴan Siyasa, Ƙungiyoyi, Manoma, Jaruman Wasan Kwaikwayo, Mawaƙa, Likitoci da Malaman Asibiti, Shuwagabannin Addinai, da ma Shuwagabannin Jama’a, da makamantansu.

Ka zalika, ta soki yadda aka gaza yabawa Gwamnatin Buharin, lokacin da ludayinta ke kan damo.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button