Ƙasashen Ƙetare

Saurayi Ya Hallaka Budurwarsa, Ta Hanyar Caccaka Mata Almakashi

Wani Saurayi, mai suna, Liam Taylor, ya amsa laifin hallaka budurwarsa, mai shekaru 28 a duniya, Ailish Walsh, ta hanyar caccaka mata Almakashi har sau 40.

Taylor ya kuma amince da hallaka budurwar tasa da ke ɗauke da ciki har na tsawon makonni 12 ne, a wani hari da ya kai gidanta, da ke Hackney, a gabashin London, bayan da ta yi yunƙurin rabuwa da shi, saboda ya na shaye-shaye, a cewar Jaridar Dailymail, ta ranar Litinin.

Bayan daƙume shi ne kuma, sai ya bayyana wa Jami’an ƴan sandan cewar, ”abin akwai ciwo yadda budurwar ke ƙoƙarin sauya rayuwarsa zuwa ta hauka”.

Ko a baya dai, an sha samun Taylor ɗin da laifukan cin zarafin mata, kafin yanzu da ya aikata kisan kai.

Kuma tuni, Mai Shari’a, Alexia Durran, ta aike da shi zuwa gidan gyaran Hali, tare da ɗage cigaba da sauraron shari’ar.

Inda ta ce : ”Ka aikata babban laifi a yau, kuma ƙasurgumi daga cikin laifuka, dan haka hukuncin wannan laifi dai guda ɗaya ne.

”Kawai dai, abin tambayar shi ne tsawon loakacin da za a ɗauka, kafin majalissar zartarwa ta cimma matsaya kan sakinka”.

Za a cigaba da sauraron shari’ar ne kuma, a ranar 10 ga watan Mayu, ya yin da har yanzu ba a sanya ranar yanke hukunci ba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button