Shagali: Yadda Bikin Cikar Auren Osinbajo Da Matarsa Shekaru 34 Ya Ke Gudana
A yau (Asabar) ne, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ke cika shekaru 34 da Angwancewa da Matarsa, Dolapo.
Osinbajo shi ne ya bayyana yadda shagalin cikar Auren nasu shekaru 34 ya ke gudana, ta hanyar wallafa hotuna da bidiyonsu, ta shafinsa na kafar sada zumunta ta Instagram, tare da rubuta cewa, “Ina godiya ga wannan muhimmiyar dama da alfarma da Ubangiji ya yi min, a yau mu ke cika shekaru 34 masu Albarka. Barka da cika shekaru 34 da zama Amarya #dolapoosinbajo! Yemi ya na ƙaunarki a ko da yaushe”.
A nata ɓangaren, ita ma Dolapo wallafa hotunan bikin cikar tasu shekaru 34 ta yi a shafinta na Instagram, tare da rubuta cewar, “Shekaru 34 cikin amincin Ubangiji, Nagodewa Ubangiji”.
Yemi da Dolapo dai, sun kasance cikin inuwa ɗaya a matsayin Ma’aurata tun shekarar 1989.