Shekaru 8 Da Buhari Ya Shafe Yana Buga Kuɗi Ne Ya Jefa Najeriya Cikin Halin Hauhawar Farashi – Ministan Kuɗi
Ministan kuɗi, Wale Edun, ya ɗora alhakin hauhawar farashin da ake fuskanta a ƙasar nan, akan buga tiriliyoyin kuɗaɗen Naira da tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi, ba tare da la’akari da alfanu ko rashin alfanun hakan ba.
Ministan, ya bayyana hakane ranar Laraba, ya yin da ya bayyana a gaban Kwamitin Kuɗi Na Majalissar Dattijai, ya na mai cewa, “za mu bincika Naira tiriliyan 22.7 da aka buga”.
Ya kuma ƙara da cewar, “Naira tiriliyan 22.7 da Babban Bankin Ƙasar nan (CBN) ya buga, ta hanyar bugawa a jibge da gwamnatin tarayya ta yi a shakarun 2015 zuwa 2023, shi ne ya tsunduma Najeriya cikin yanayin hauhawar farashin da ake fama da shi.
A jawabinsa na rufe zaman tattaunawar, shugaban kwamitin, Sanata Sani Musa, na jam’iyyar APC daga Niger ta Gabas, ya ce zaman tattaunawar abu ne da za a cigaba da gudanarwa, har sai an samar da hanyoyin fitar da a’i daga rogo game da halin da tattalin arziƙin Najeriya ya tsinci kansa.