Shirin Labarina Ya Sauya Min Tunani – A Cewar Raba Gardama
Fitaccen jarumi a masana’antun shirya fina-finan Arewaci da na Kudancin Najeriya (Kannywood & Nollywood), Adam Garba, da aka fi sani da ‘Raba Gardama’ a cikin shirin Labarina, na kamfanin Saira Movies, ya bayyana cewar, shirin na Labarina, ya sauya masa tunaninsa game da rayuwar al’ummar Arewa, inda ya bayyana cewar, ya ji daɗin Aikin shirin, masu ɗaukar shirin, da ma labarin Shirin baki ɗaya.
Raba Gardama, ya bayyana hakan ne, ya yin da ya ke zantawa da shafin BBC Hausa, ta cikin shirin ‘Daga Bakin Mai Ita’ a yau (Alhamis).
Jarumi Adam dai, ya bayyana cewar, Shirin na Labarina, shi ne shirinsa na biyu a Masana’antar Kannywood, bayan shirin Kwana Casa’in da Darakta Salisu T. Balarabe, ya gayyace shi.
Ka zalika, ya ce Abokinsa, Isah Peroskan, da aka fi sani da Presidor na shirin Labarina ɗin ne ya gayyace shi, domin shiga cikin tantancewar masu sha’awar taka wannan rawa, inda kuma bayan gwadawa, Daraktan shirin ya amince da ƙwazonsa.
Ya kuma ce, sam cecekucen ababen da Jama’a ke faɗa game da rawar da ya taka a cikin shirin bai dame shi ba, domin kuwa abu ne da Jarumai su ke shan gamuwa da shi.
“Cecekuce bai dame ni ba, saboda komai ka yi a rayuwa sai wani ya kushe, musamman ma a wurinmu Jarumai”, a cewarsa.
Da aka yi masa tambaya kan banbancin da ke tsakanin Fina-finan harshen Hausa da na Turanci kuwa, sai Jarumin ya ce, Kayan Aiki da Kuɗin Aiki ne banbancinsu.