Labarai
Shirye-Shirye Sun Yi Nisa Domin Farfaɗo Da Samar Da Ruwan Sha A Jihar Nasarawa
Gwamnan jihar Nasarawa, Engr. Abdullahi A. Sule, ya gudanar da zaman tattaunawa da Masana, kan yadda za a farfaɗo da tsarin samar da ruwan sha a Gudi, Mandara, da Keffi da ke jihar.
Aikin farfaɗo da tsarin ruwan Shan kuma, na daga cikin shirye-shiryen Gwamnatin jihar na faɗaɗa wadatuwar ruwan sha, a faɗin jihar.
An gudanar da taron ne kuma, jiya (Alhamis), 16 ga watan Nuwamban da mu ke ciki, a gidan Gwamnan jihar ta Nasarawa, da ke Asokoro, a babban birnin tarayya Abuja.