Shugaba Tinubu, Ya Bada Umarnin Ƙaddamar Da Bincike Kan Yawaitar Haɗuran Jirgin Ruwa
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bada umarnin ƙaddamar da bincike kan yawaitar samun haɗuran jiragen ruwa, a ƙasar nan.
Shugaban ya bada wannan umarni ne, ga hukumomin kula da albarkatun ruwa, biyo bayan haɗurran jiragen ruwan da aka yi ta fuskanta, a jihohin Adamawa, da Niger.
Idan za a iya tunawa dai, aƙalla mutane 24 ne su ka rasa rayukansu, bayan da wani jirgin ruwa ya tuntsure a Gbajibo, da ke yankin Mokwa a jihar Niger, ranar Lahadi.
A ƙauyukan Njuwa, Rugange, da ƙaramar hukumar Yola ta Kudu ma dai, aƙalla mutane takwas ne su ka rasa rayukansu, inda wasu mutane bakwai su ka yi ɓatan dabo, bayan tuntsurewar jirgin ruwa.
Ya yin da yake miƙa saƙon taáziyyarsa ga Iyalan waɗanda su ka rasu, shugaba Tinubu, ya yi fatan samun lafiya, ga waɗanda su ka samu raunuka.