Labarai

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sarki Charles

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da Sarkin Burtaniya, King Charles na III, a ya yin taron COP28 da ya ke gudana, a Dubai.

Shugaba Tinubu, ya wallafa hoton ganawar tasu da Sarki Charles ne ta shafinsa na Instagram, a ranar Alhamis, ya na bai bayyana cewar, sun tattauna ne kan yadda za a ƙara ƙulla alaƙa a tsakanin ƙasashen biyu.

Inda rubutun da aka wallafa tare da hotunan ke cewa, “Na samu ganawa da Maimartaba Sarki Charles III na Burtaniya, wanda shima shugaban ƙasashen yankin Turai masu ƙarfin tattalin arziƙi ne.

“Tattaunawar tamu kuma wani mataki ne na ƙara ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Tarayyar Turai, Kuma na yi farinciki matuƙa da kyakykyawan sakamakon da ganawar tamu za ta samarwa yankunanmu a nan gaba, a cigaba da ƙoƙarin da mu ke na inganta dangantaka da alaƙarmu a ya yin taron na #COP28”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button