Shugaba Tinubu, Ya Yabawa Shugaban Hukumar JAMB, Bayan Tarawa Gwamnati Naira Biliyan 50
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yaba da jagorancin shugaban hukumar shirya jarrabawar neman shiga manyan makarantu ta ƙasa (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyede.
Shugaban ya bayyana wannan yabo ne, ya yin da ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima, a taron jin ta bakin al’umma da hukumar EFCC ta shirya, a babban birnin tarayya Abuja.
Shugaba Tinubu, ya ce tun da aka samar da hukumar bata taɓa rabauta da jagora mafi ƙwazo kamar Oloyode ba, haka zalika babu wanda ya taɓa tarawa Gwamnati Naira biliyan 50 daga hukumar, a cikin shekara guda.
Baya ga haka, shugaban ya ƙara da jaddada yadda ƙasar nan ke fatan rabauta da mutane masu ƙwazo da mayar da hankali kan aiki, irinsu Farfesa Oloyoden.
A ƙarshe ya kuma ya yi kira a gare shi da ya ninka jajircewarsa, tare da ƙara ƙaimi kan aniyarsa ta cicciɓa hukumar.