Shugaban Jam’iyya Ya Lakaɗa Wa Kwamishiniya Dukan Kawo Wuƙa, Kan Rabon Kayan Rage Raɗaɗi
An kaiwa Kwamishiniyar al’amuran Mata da bunƙasa cigaban Jama’a, ta jihar Ondo, Mrs Adebunmi Osadahun hari, kan rabon kayayyakin Rage Raɗaɗi na Gwamnatin tarayya, a ƙaramar hukumar Akoko ta Arewa.
Ana zargin Shugaban jam’iyyar APC, Olumide Awolumate ne dai, da aikata wannan ta’asa, bayan da ya zargi Kwamishiniyar da cire sunansa daga jerin sunayen waɗanda za su amfana da kayan rage raɗaɗin a Arigidi.
Wani fai-fan bidiyo da ke cigaba da zagayawa a kafafen sada zumunta na zamani, ya nuna yadda Shugaban jam’iyyar wanda aka fi sani da Cuba, ya naɗe gwuiwar hannu ya na tumar Kwamishiniyar a bainan-nasi.
Da kuma ta yi yunƙurin tsira daga azabar ta Cuba, sai ya yi amfani da kujera wajen kwaɗa mata a ka, tare da yunƙurin ɗaukar teburin da ke wurin, kafin daga bisani ya dakata.
A cikin bidiyon, an kuma hangi yadda kan kwamishiniyar mai ƙarancin gashi ya kumbura.
Wata majiya, ta bayyana cewar, Awolumate, wanda shi ne Shugaban jam’iyyar APC na ɗaya na wannan mazaɓa, ya aikata wannan aika-aika ne cikin fusata, bisa zargin cire sunansa daga jerin waɗanda za su amfana da tallafin rage raɗaɗi na Gwamnatin tarayya.
Tuni kuma Jami’an ƴan sanda su ka cika hannunsu da Shugaban jam’iyyar, a birnin Ondo, bayan da Kwamishiniyar ta shigar da rahoton ƙorafi ga Ofishin Baturen Rundunar Ƴan Sanda, inda aka bayyana mata cewar ba ya nan.
Majiyarmu ta kuma bayyana yadda Jami’an ƴan sandan su ka gaza taɓuka komai, a ya yin da lamarin ya ke aukuwa.
A makon da ya gabata ne dai, Gwamnatin jihar ta Ondo, ta fara rabon kayayyakin tallafin rage raɗaɗi ga Magidanta, inda aka buƙaci Kwamishinoni da su jagoranci rabon, a yankunan ƙananan hukumomin su.
Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Bamidele Ademola-Olateju, ya ce za a raba Buhunhunan Shinkafa guda 1,200 ne, ga Magidanta 6,000 a yankunan da ke jihar.