Zamantakewa

Shugaban Majalissar Dokokin Niger, Zai Aurar Da Marayu 100 Da Ƴan Bindinga Su Ka Raba Da Iyayensu

Shugaban Majalissar Dokokin jihar Niger, Abdulmalik Sarkindaji, ya bayyana shirinsa na Aurar da Mata Marayu 100, da su ka rasa Iyayensu, a harin da Ƴan Bindinga su ka kai ƙaramar hukumar Mariga.

Sarkindaji, ya bayyana hakan ne ga manema labarai, a birnin Minna, babban birnin jihar, a ranar Juma’a.

Shugaban, ya yi alƙawarin biyawa Ƴan Matan kuɗin Aure, tare da saya musu dukkannin kayayyakin da ake buƙata, na bikin Aure.

An kuma zaɓo ƴan matan da za a Aurar ɗin ne, daga cikin jerin ƴan mata 170 da aka miƙawa shugaban majalissar sunayensu.

Sarkindaji ɗin, ya sanar da hakan ne, ba tare da bayyana adadin shekarun marayun ba.

Shugaban Majalissar, wanda kuma Ɗan Majalissa ne, da ke wakiltar Mariga, ya ce wannan Aiki, ya na daga cikin ayyukansa na mazaɓa.

Sarkindaji, ya ce Gwamnan jihar, Mohammed Umar Bago, da Sarkin Kontogora, Alhaji Mohammed Barau ne za su kasance waliyyan Ƴan Matan, a yayin wannan Auren gata.

Ana kuma sa ran Shugaban hukumar HISBAH ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, zai samu halartar bikin, wanda za a gudanar ranar 24 ga watan Mayun da mu ke ciki, a Bangi, helikwatar ƙaramar hukumar Mariga.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button