Labarai

SSANU Da NASU Na Barazanar Tsunduma Yajin Aiki

Kwamitin gamayyar ƙungiyoyin Manyan Ma’aikatan Jami’o’i (SSANU), da Ma’aikata waɗanda ba Malamai ba (NASU) ya yi barazanar kawo cikas a cikin harkokin Jami’o’in ƙasar nan, muddin Gwamnati ta gaza biyan membobinsu kuɗaɗen albashinsu da ta riƙe.

Tsohuwar gwamnatin, Muhammadu Buhari ce dai ta riƙe Albashin Ma’aikatan, ya yin wani ‘Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani’ da su ka gudanar, a shekarar 2022.

Ta cikin wata wasiƙa da Kwamitin gamayyar ƙungiyoyin ya fitar, a ranar Juma’a, da ke ɗauke da sa hannun shugaban SSANU, Muhammed Ibrahim, da Babban Sakataren NASU, Peters Adeyemi, sun ƙalubalanci gwamnati kan biyan Albashin membobin ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) na watanni huɗu, ya yin da ta gaza biyan nasu membobin albashinsu.

Ƙungiyoyin sun kuma ce, bai zama lallai Jami’o’i su cigaba da zama lafiya ba, muddin gwamnati bata biya ƙungiyoyin kuɗaɗen albashin da su ke binta ba.

Kafin hakan kuma, ƙungiyoyin sun aike da wasiƙar gudanar da zanga-zanga ga Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, da Ministan Ilimi, Tahir Mamman, tun a ranar 13 ga watan Fabrairun da ya gabata, sakamakon tsame ma’aikatan da ba Malamai ba, daga biyan albashin na watanni huɗu.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button