Ilimi

SSANU Za Ta Ƙaddamar Shirin Aure A Tsakanin Membobinta

Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’i ta SSANU, reshen Jami’ar Bayero da ke Kano, na shirye-shiryen ƙaddamar da tsarin Auren cikin gida, a tsakanin Membobinta.

Bayanin hakan ya fito ne ta bakin Shugabar Matan ƙungiyar, reshen BUK, Farida Sani Kamba, a ranar Alhamis, ya yin buɗe taron Matan ƙungiyar reshen Jami’ar Bayero.

Inda ta ce, Auren wani ɓangarene daga cikin ƙoƙarin ƙungiyar na ganin ta ƙara ƙarfafa alaƙa a tsakanin Membobinta.

“Wannan shiri zai samu kaiwa ga gaci ne kawai idan muka samu goyon bayan membobinmu Maza da Mata. Wasu daga cikinmu kuwa daman tuni sun yi irin wannan Aure na cikin gida da waɗanda mu ke Aiki tare da su, Abu ne kawai da ya ke ƙara ƙarfafa zumunci”, a cewar Kamba.

A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar ta SSANU reshen Jami’ar Bayero, Comrade Mustapha Aminu, ya ce ƙungiyar za ta yi dukkannin mai yiwuwa wajen ganin ta bunƙasa walwalar membobinta, a ƙarƙashin kulawarsa.

Ya kuma ce akwai tsare-tsare da dama da ƙungiyar ta bijiro da su, domin tallafawa membobinta, kamar ƙananan basussuka, tallafin kula da lafiya, bada tallafin karatu ga Yara, da makamantansu.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button