Wasanni

Super Falcons Za Ta Kece Raini Da Kamaru, Kafin Samun Tikitin Wasannin Olympics

Hanyar riskar wasan Olympic na mata, a shekara mai zuwa, ga tawagar Kwallon Kafar Kasar nan, wacce ta sha lashe gasar har karo tara, na dauke da kalubalen fafata wasa da kasashen Ghana da Kamaru, biyo bayan tashi wasa cancaras da tawagar ta yi, da yammacin ranar Talata, a birnin Cairo.

Bayan haduwar su da kasar Ethopia, a rukuni na biyu na neman cancantar buga gasar da za a gudanar cikin watan Oktoban shekarar da mu ke ciki, ana sa ran Falcons zata buga wasa tsakaninta da wacce ta kasance zakara, cikin kasashen Uganda ko Rwanda, da kuma kasar Kamaru.

Idan kuma ta samu saár shallake shingen na Kamaru, Tawagar Matan na Najeriya za ta sake gwabzawa da gwarzuwa tsakanin kasashen Guinea Bissau ko Jamhuriyyar Benin, da ma Guinea da Ghana.

Idan masu sauraro za su iya tunawa dai, kasar Kamaru ta taba hana tawagar ta Najeriya samun cancantar buga wasannin Olympics na shekarar 2012, da aka gudanar a birnin London, bayan da ta doke ta da kwallo biyu, a bugun Fenareti, a birnin Yaounde.

Ita ma Equatorial Guinea ta taba dakatar da Super Falcons din, daga samun damar shiga wannan gasa, a shekarar 2016.

Sai dai ita ma Super Falcons din, ta sha dakatar da Indomitable Lionesses daga samun tikitin halartar gasar kofin duniya, wanda ya hadar da buge su da tayi a wasan dab da na kusa dana karshe na gasar Kofin kwallon kafar matan Afirka, da aka gudanar a shekarar da ta gabata, a kasar Morocco.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button