Kasuwanci

Talaucin Da Ake Fama Da Shi A Najeriya Ya Ragu Da Kaso Bakwai Cikin Ɗari – A Cewar Bankin Duniya

Bankin Duniya, ya bayyana cewar, damarmakin da aka dinga rabauta da su ta hanyar Intanet, a tsawon shekaru uku da su ka gabata, sun taka gagarumar rawa wajen rage yawan talaucin da ake fama da shi a ƙasashen Najeriya da Tanzaniya, da kaso bakwai.

Hakan kuma na ƙunshe ne, ta cikin wani gajeren jawabi da bankin ya fitar, mai taken, “Tasirin Sauyawar Zamani Zuwa Fasahar Zamani, Ga Cigaban Afirka”, inda bankin ya ce, lamarin ya kuma ƙara yawan samun ayyukan yi, da kaso 8.

Bankin na Duniya, ya ce “a shekarar 2023, rahoton bankin duniya ya gano yadda ƙasashen Najeriya da Tanzaniya, su ka samu ƙaruwar fama da talauci, a shekaru ukun baya, ya yin da a shekaru ukun gaba kuwa, sakamakon bayyanar Intanet, sai a ka samu raguwarsa, tare da ƙaruwar ayyukan yi, da sama da kaso takwas”.

A nasa ɓangaren, Ministan sadarwa da cigaban tattalin arziƙin zamani na Najeriya, Dr Bosun Tijani, ya ce farashin awar sadarwa (Data) a Najeriya, ya na daga cikin mafiya araha a faɗin duniya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button